Makamai Masu Linzami Na Kasar Yemen Ta Fada Kan Tashar Jaragen Sama Na Ben Gurrion

Majiyar sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami sanfurin Bilistic kan tashar jiragen sama mafi cinkoso da ke birnin

Majiyar sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami sanfurin Bilistic kan tashar jiragen sama mafi cinkoso da ke birnin Yafa ko Tel’aviv, wanda na farko ya tilastawa jiragen sauka da dashi a tashar. Sannan miliyoyin mutane suka ruga zuwa mabuya saboda tsaron kansu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin sojojin kasar ta Yemen Burgedia Janar Yahayah sari yana fadar haka.

Yahayah Saree ya kara da cewa sojojin kasar sun yi amfani da makamin bilistic Hiphasonic Palastine 2 a wannan harin kuma ya sami bararsa kamar yadda aka tsara.

Jaridar HKI ta Calcalist,   ta bada labarin cewa wani jirgi wanda ya taho daga Dubai yayi ta shawaje a yankin saboda bayan an cilla makamin daga kasar yemen, zuwa wani lokacin kafin ya sauka. Haka ma sauran jiragen da suke son sauka a tashar sun yi ta shawagi na kimanin mintoci 30 kafin a basu izinin sauka. A

Wata jiridar HKI mai suna Hayom ta bada labarin cewa an rufe tashar jiragen sama ta Ben Guriom na tsaawon mintoci 30 kafin a sake bude ta.

San’a dai ta sha alwashin rufe tashar jiragen na Bengurrion da kuma hana jiragen ruwa HKI ko masu zuwa cn wucewa ta tekun red sea matukar HKI ta ci gaba da kashe mutanen Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments