Majalisar dokokin Iran ta amince da Ali Madinizadeh, wanda shugaba kasar Pezeshkian ya gabatar a mukamin ministan harkokin tattalin arziki da kudi na kasar.
‘Yan majalisar dokokin Iran sun amince da nadin masanin tattalin arziki mai shekaru 43 a mukamin da kuri’u 171, yayin da 67 suka ki amincewa da shi, sannan 8 daga cikin 246 na majalisar Musulunci ta Iran suka ki kada kuri’a.