Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kai hare-hare har sau uku kan cibiyoyin leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila
Ma’aikatar hulda da jama’a ta dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta bayyana harin da aka kai kan cibiyoyin leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila a mataki na uku na hare-haren daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na Uku”.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa: Hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suke kaiwa kan kasar Iran da jijjifin safiyar yau sun nufi yankunan gidajen jama’a ne. Sannan maharan yahudawan sahayoniyyan sun kashe jami’an leken asirin dakarun kare juyin juya hali uku, shahid Mohammad Kazimi, Hassan Mohaqeq, da Mohsin Baqiri.
A ci gaba da mayar da martani kan laifuffukan ta’addancin yahudawan sahayoniyya, Dakarun kare sararin samaniyar kasar Iran na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kai wani sabon harin makami mai linzami kan cibiyoyin leken asiri na ‘yan sahayoniyya a mataki na uku hare-haren daukan fans ana “Alkawarin Gaskiya na Uku”.
Hakika Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta lashi takwabin ruguza duk wani muhimman wuri da cibiyar aikata muggan manufofin yahudawan sahayoniyya kafin kawo karshen wannan yaki da gwamnatin haramtacciyar kasar kasar Isra’ila ta daura kan Iran.