Sojojin kasar Iran sun yi gargadi ga Isra’ilawa mazauna yankunan da aka mamaye, su gaggauta ficewa a daidai lokacin da Iran ke shirin kaddamar da hare-hare a yankin.
A cikin wani sako da aka watsa ta gidan talabijin, Kanar Reza Sayyad, kakakin cibiyar sadarwa ta sojojin kasar ta Iran, ya gargadi mazauna yankin da cewa ci gaba da zama a yankin zai jefa rayuwarsu cikin hadari, a daidai lokacin da Iran ke mayar da martani kan harin da sojojin Isra’ila suka kai a baya-bayan nan.
Kanal Sayyad ya yi Allah wadai da gwamnatin Netanyahu yana mai cewa matakin da Iran za ta dauka zai kara fadada a duk sassan yankunan da Isra’ilar ta mamaye.
Sojojin Iran, in ji Sayyad, suna da “cikakkun bayanai ne leken asiri” kan wasu muhimman wurare a yankunan da Isra’ila ke iko da su, yana mai gargadin mazauna yankunan da su guji wadannan wuraren tare da lura da cewa ko matsugunan karkashin kasa ba zasu ba da tabbacin tsaron lafiyarsu ba.
Kalaman Sayyad ya biyo bayan wani sabon harin makami mai linzami da jirage marasa matuka da dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) suka kaddamar a yammacin Lahadi a wani bangare na Operation True Promise III.