Jaridar “Maariv” ta buga labarin da yake cewa; Tattauanwa a tsakanin “Isra’ila” da kasashen Afirka akan yadda za su bayar da dama ga mutanen Gaza da su yi hijira zuwa can, ta yi isa sosai.
Rahoton jaridar na jiya Juma’a ya ci gaba da cewa; Tattaunawar ana yinta akarkashin damar da za a bai wa Mutanen Gaza su yi hijira cikin zabin kansu, zuwa wasu kasashen na Afirka, kuma Amurka tana cikin wadanda ake tattaunawar da ita da wadannan kasashen na Afirka. Haka nan kuma jaridar ta ‘yan sahayoniya ta ce, kasashen da ake tattaunawa da su, sun nuna amincewarsu a matakin na farko ka karbar bakuncin mutanen Gaza.
Tattaunawar dai ta kunshi yadda za a gina matsugunan Falasdinawan da za su yarda su yi hijirar, da kuma makarantunsu.