Iran ta sanar da cewa an sauya ranar tattaunawa karo ta hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington da Tehran a ranar Asabar mai zuwa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba tsakanin Iran da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Rome na kasar Italiya.
Esmail Baghai ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne bisa bukatar ministan harkokin wajen kasar Oman, kuma Za a sanar da sabon lokaci nan gaba.
Baghaei ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da hanyar diflomasiyya wajen kare muradun al’ummar Iran da kuma kawo karshen takunkumi da matsin tattalin arziki da ke shafar hakkokin bil’adama da jin dadin al’ummar Iran.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, Iran za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a cikin wadannan shawarwari.