Amurka Da Ukraine Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyar Da Aka Dade Ana Saurarunta Dangane Da Ma’adinai

Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan

Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata.

Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa yawan kudaden da Amurka ta tallafawa Ukraine a yakin dai ya kai dalar Amurka biliyon $175, kuma wannan ita ce hanya tilo wacce Ukraine zata iya biyan wadannan basussuka.

Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjeniyar. Wannan na faruwa ne al-hali ana ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Wannan yarjeniyar dai ta tabbatarwa Rasha kan cewa akwai yiyuwan a samar da zaman lafiya a kasar ta Ukraine, don ba yadda za’a yi a fidda wadan nan ma’adinai masu tsada a kasar Ukraine tare da ci gaba da yaki a kasar.

Kasar Rasha dai ta sanya sharudda na tsada yaki a Ukraine, wadanda suka hada da amincewa da halin da ake ciki tsakanin kasashen biyu, wato yankin Cremea da Dambas wadanda Rasha ta mamaye tun farkon yakin sun zama bangaren kasar Rasha har’abada, Ukrain ba zata shigo kungiyar tsaro ta Nato ba da kuma tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments