Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun

Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila

Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9.

Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar da cewa suna ci gaba da gudanar da mummunan arangama a tsawon kusan watanni biyu da kuma kalubalantar hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen a matakin mayar da martani da kalubalantar hare-haren wuce gona da iri kan kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments