News Fox: Sau 6  Yemen Ta Kakkabo Jiragen Amurka Samfurin Mq 9 A Karkashin Gwamnatin Trump

Tashar talbijin din “News Fox” ta kasar Amurka  mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ta watsa wani rahoto da yake cewa; Daga lokacin da Donald Trump

Tashar talbijin din “News Fox” ta kasar Amurka  mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ta watsa wani rahoto da yake cewa; Daga lokacin da Donald Trump ya zama shugaban kasa, sau 6 sojojin Yemen su ka kakkabo jiragen sama maras matuki samfurin Mq9.

Rahoton na tashar talabijin din Fox ya kuma yi ishara da yadda sojojin na Yemen su ka kakkabo jirgin sama marasa matuki da marecen juma’a, wanda shi ne karo na 6 tun daga ranar 3 ga watan Maris.

Rahoton ya kuma kara da cewa; Kowane daya daga cikin jiragen sama marasa matuki  samfurin mq9 ya kai dalar Amurka miliyan 30.

 Bugu da kari rahoton ya kuma bayyana cewa; Sau 35 sojojin Amurka suna kai wa kasar Yemen hare-hare, amma kuma duk da haka har yanzu  sojojin Yemen suna ci gaba da kai wa wadannan jiragen na Amurka masu tsada hari. Haka nan kuma sojojin na Yemen suna ci gaba da hana wucewar jiragen  ruwa da suke zuwa HKI.

Wannan rahoton kuma ya yi ishara da yadda sojojin na Yemen suke kai wa HKI hare-hare da makamai masu linzami masu cin dogon zango. 

Daga fara kai farmakin Aksa zuwa yanzu, adadin jiragen Amurka samfurin  MQ 9 da sojojin yemen su ka kakkabo sun kai 16, sai dai wata majiyar ta bayyana cewa, jiragen da sojojin na Yemen su ka kakkabo sun kai 20. Wani jami’in ma’aikatar tsaro ta kasar Amurka ya sanar da tashar talbijin din ta Fox cewa; A 2024 Amurka ta kera, jragen MQ 9 guda 230, amma a kasar Yemen kadai an harbo 16 daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments