Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa
A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher.
Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar kan shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher.
Majiyar ta tabbatar da cewa artabun ya yi sanadin lalata motocin yaki guda 15, da motocin dakon mai. Ta kuma tabbatar da cewa, an samu nasarar lalata da dama daga cikin motocin mayakan Dakarun Rapid Support Forces ciki har da manyan jami’an rundunar da yawansu ya haura 70 da suka hada da kwamandoji da dama baya ga wani adadi mai yawa da suka jikkata, yayin da sauran suka gudu, inda suka bar matattu da wadanda suka jikkata a filin daga.