Amurka Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare Kan Garuruwan Sana’a, Sa’adah Da Al-Jawf Na Kasar Yemen

Kasar Yemen ta sanar da cewa: Amurka ta kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan garuruwan Sana’a, Sa’dah, da Al-Jawf Mahukuntan Yemen sun

Kasar Yemen ta sanar da cewa: Amurka ta kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan garuruwan Sana’a, Sa’dah, da Al-Jawf

Mahukuntan Yemen sun sanar da cewa: Amurka ta ci gaba da kai hare-hare kan kasar Yemen, inda ta kaddamar da wasu jerin hare-hare kan garuruwan Sana’a, Sa’dah da Al-Jawf.

Wakilin Al-Alam ya ruwaito a yammacin jiya Juma’a cewa: Jiragen saman yakin Amurka sun kaddamar da hare-hare har sau shida a gundumar Bani Hushaysh dake arewa maso gabashin birnin Sana’a fadar mulkin kasar Yemen, inda suka yi luguden wuta a wurare da dama.

A lardin Al-Jawf, an kai wasu hare-hare 4 ta sama a gundumar Bart Al Anan da yankin Al-Yatmah da ke gundumar Khab da gundumar Al Sha’af a arewa maso gabashin kasar Yemen.

A ranar alhamis din da ta gabata, rundunar kawancen da Amurka ke jagoranta ta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan birnin Al-Hodeida, inda suka yi ta kisan kiyashi kan fararen hula da ma’aikata a tashar Ra’as Issa da ke birnin. Hare-hare 14 ne suka kai kan cibiyoyin tashar jiragen ruwa da tankunan mai da iskar gas, inda suka kashe fararen hula fiye da 80 tare da raunata wasu 160, bisa ga kididdigar farko, a cewar ma’aikatar lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments