Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Sabbin Hare-Hare Kan Kasar Yemen A Daren Jiya

Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar. Tashar talabijin ta

Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har  13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har da Yankunan  Malikah da Sarf na birnin San’aa babban birnin kasar.

Wasu kafafen yada labaran kasar Yemen sun bayyana cewa, kafin haka jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a kan kasar ta Yemen wadanda suka kai ga shahadar fararen hula 12 da kuma raunata wasu 2 a birnin San’aa babban birnin kasar.

Washington ta bada sanarwan cewa ta na kai hare-haren don tabbatar da tsaron jiragen ruwan kasuwanci da suke wucewa a tekun red Sea. Alhali gwamnatin kasar Yemen ta ce tana kai hare-hare kan jiragen ruwan HKI ko masu zuwa HKI ne kawai. Sauran jiragen ruwan kasuwanci suna wucewa ba tare da wata matsala ba.

Banda haka sojojin kasar Yemen sun maida martanin hare-haren da Amurka take kaiwa kan kasar, tare da cilla makamai masu linzami kan jiragen yakin Amurka da na HKI a tekun re sea da kuma tashar jiragen sama ta Bengerion a HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments