Wani Asbiti A Amurka Ya Kori Wata Likita Daga Aiki Bayan Ta Yi Allawadai Da Yahudawan Sahyoniyya

Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar

Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46 a duniya, ta aika sako cikin shafinta na yanar gizo inda take goyon bayan kungiyoyin Hamas da Hizbullah na kasar Lebanon sannan tana allawadai da kuma aibata HKI kan kissan yara da take yi a Gaza.  

Gwamnatin kasar Amurka dai tana ganin kanta a matsayin kasa wacce take gaba wajen kare hakkin fadin albarkacin baki, amma idan al-amarin ya shafi HKI sai ta nuna fuska biyu. Ta kuma kareta ido a rufe kamar sauran Amurkawa da kuma kasashen duniya basa kallo.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa yanzu sojojin HKI ta kashe falasdinawa akalla dubu 50 a gaza kashi 2/3 daga cikinsu mata da yara ne.

Sannan abin ya yi muni inda gwamnatin Amurka ta tsaya gaban kotun ICC wacce ta tabbatar da laifukan HKI, ta kuma bada sammacin kama Firai ministan HKI da tsohon ministan yakin sa Yoav Galant. Inda ta kakabawa jami’an kotun takunkuman tattalin arziki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments