Jagoran Juyin juya halin musulunci a nan Iran yace, watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo da ni’imomi masu Yawa waannda matasa da sauran mutanen kasar suka amfani da su,kuma sun hada da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’ii mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu.
Amma a wani bangare a cikin wannan Ramadan, duk tare da jin dadin da muka samu, amma watan yana tattare da dacinsa, kissan mutanen Falasdinu, tare da goyon bayan Amurka.
Kasashen yamma suna tuhumar Iran da cewa tana amfani da sojojinta a yankin don rikita yankin, amma gaskiyar al-amarin, su suke da wakiliya a wannan yakin, kuma itace HKI, wacce take wakiltansu a ayyukan ta’addanci da take yi a kasashen Falasdinu, Siriya iran da sauransu.
Idan Falasdinawa sun tashi suna kare kasarsu sai su ce ai yan ta’adda ne, alhali sune yan ta’adda da gaskiya.
Ayyukan HKI a yankin sun hada da kashe masana a cikin gaza, Iraki , Lebanon Iran da sauransu suna kashesu don kada wadannan kasashe su ci gaba.
Jagoran ya kara da cewa: Muna ganin yadda matasa a kasashen yamma suke fitowa kan tituna Suna nuna rashin amincewarsu da abinda kasashen yamma tare da amfani da HKI suke yi a Gaza, wannan ya nuna ba su san abinda yake faruwa tun da dadewa wa ba, da sun sani fiye da haka, da za su kara tashin kan gwamnatocinsu.
Sannan idan wadannan kasashe sun yi kokarin tada fita a cikin kasa to mutanen kasar zasy yi maganinsu.