Search
Close this search box.

Dakarun Al-Kassam Sun Sami Nasarar Halaka Sojojin HKI A Kudancin Gaza

Mayakan dakarun Izzuddin Kasam rahen soje na kungiyar Hamas sun bada sanarwan halaka sojojin HKI a kudancin Gaza, a wani tarkon mayakan da suka fada

Mayakan dakarun Izzuddin Kasam rahen soje na kungiyar Hamas sun bada sanarwan halaka sojojin HKI a kudancin Gaza, a wani tarkon mayakan da suka fada ciki.

Kamfanin dillancin labaran SAMA ya nakalto wani bayanin da dakarun Izzudden Kassam suka fitar a safiyar yau Litinin na cewa, a wannan takon sun halaka ko raunata akalla sojojin HKI 5.

Bayanin ya kara da cewa dakarun Kassam sun yi amfani da makami mai linzami samfurin TBG wajen tarwatsa wani gidan da sojojin HKI suka boye a ciki a garin Khan Yunus. Banda haka bayanin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun fada wani tarkon dakarun a gabacin Khan Yunus, inda suka shiga wani ramin da Falasdinawa suka tona suka kuma bisne nakiya a kofar shigarta, inda a nan ma suka tada nakiyar wacce ta halaka ko ya jikata sojojin yahudawan.

A wani labarin kuma wata majiyar sojojin yahudawan HKI ta tabbatar da cewa an kashe sojan HKI guda a kudancin Gaza.

Wannan ya kawo adadin sojojin yahudawa wadan gwamnatin kasar ta tabbatar da halakarsu a Gaza zuwa 702 sannan wasu 4,378 suka ji rauni.

Wannan tare da sanin cewa adadin sojojin HKI da suka halaka sun fi wannan adadin saboda HKI tana boye gaskiya don hana matsalolin cikin gida.

Banda haka gwamnatin yahudawan basa fadar yawan sojojin HKI wadanda kungiyar Hizbullah take halakasu a arewacin kasar falasdinu da aka mamaye kwatakwata.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments