Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aikata munanan laifuka a kan fursunonin Falasdinawa da take tsare da su
Ma’aikatar kula da fursunonin Falasdinu ta yi Allah wadai da munanan laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a gidajen yarin da suke tsare da Falasdinawa, tana mai kira ga kasashen duniya da su bude babban bincike kan laifukan da ake aikatawa fursunoni Falasdinawa da ake tsare da su.
Kamar yadda ma’aikatar da sanar da cewa: Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi ga Falasdinawa da kuma mamaye yankunan mafiya girma a sassa daban-daban na Zirin Gaza.
Sannan wasu Falasdinawa shida da suka hada da mata biyu sun yi shahada sakamakon luguden wuta da jiragen saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan gidajen fararen hula da suke yankin Khirbet al-Adas da ke gabashin Rafah da kudancin Zirin Gaza da kuma wasu yankuna na garin Jabaliya.