Search
Close this search box.

Daliban Jami’o’i A Kasashen Duniya Suna Ci Gaba Da Bukatar A Kawo Karshen Kisan Kiyashi Ga Falasdinawa A Gaza

Daliban Jami’o’i a kasashen duniya da dama suna ci gaba da zanga zangar bukatar a kawo karshen kissan kiyashin da ake wa Falasdinawa a zirin

Daliban Jami’o’i a kasashen duniya da dama suna ci gaba da zanga zangar bukatar a kawo karshen kissan kiyashin da ake wa Falasdinawa a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS na kasar Iran ya bayyana cew a jiya Asabar,  daliban jami’o’i  daban daban a kasar Chille sun fito kan tituna a birane daban daban na kasar, suna kira da a kawo karshen kissan kare dangin da ke faruwa a gaza.

A kasar Jamus kuma wasu daliban jami’o’in sun fito zangfa zangar bukatar a kawo karshen kissan kare dangen da ke faruwa a Gaza, sun kuma bukci gwamnatin kasar Jamus ta dakatar da duk wani tallafin makaman da take bawa HKI, wacce take kashe al-ummar Falasdinu a gaza da su.

Har’ila yau an nakalto labarin bayyana cewa daliban jami’o’ii a biranen Cambera n akasar Australia da kuma  da Seul na kasar Korea ta kudu duk sun fito kan titunan kasar suna allawadai da kissan Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments