Iran Tayi Tir Da Shirin Shugaban Amurka Na Sake Tsugunar Da Al’ummar Gaza

Kakakin gwamnatin kasar iran Fatime mohajerani ta yi tir da aniyar  shugaban Amurka Donald trumph na kwashe alummar gaza zuwa wasu  wurare, kuma ta biyyana

Kakakin gwamnatin kasar iran Fatime mohajerani ta yi tir da aniyar  shugaban Amurka Donald trumph na kwashe alummar gaza zuwa wasu  wurare, kuma ta biyyana shi a matsayin ci gaba da siyasar kisan kare dangi kan alumma falasdinu,

Shugaban na Amurka Donald trump yayi wannan bayanin ne a taron manema  labarai  da yayi a fadar white hause da fira ministan isra’ila binjamin natanyaho a watan jiya, inda ya nuna aniyarsa ta kwashe alumma yankin gasa zuwa wasu kasashen larabawa. Tare da gina wajen shakatawa da babbar tashar jiragen ruwa a wajen.

Shuwagabannin  kasashen laraba wa da na musulmi sun jadda mastayinsu na amincewa da yancin falasdinawa tare da yin watsi da duk wani yunkuri na rabasu da gidajensu.

Wasu masharhanta na ganin shirin na Amurka zai jawo a mata mayar da ita saniyar ware a harkokin diplomasiya har ma tsakaninta da sauran kawayenta a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments