Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a kan Falasdinawa a arewacin zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran Mehr na JMI ya bayyana cewa hare haren sojojin HKI a arewacin yankin Gaza, yana ci gaba baba kakkautawa.
Labarin ya kara da cewa duk tare da ziyarar da wata tawagar hukumar lafiya ta duniya ta kai wasu asbitoci a yankin Gaza, sojojin HKI sun ci gaba da yin kawanya ga asbitoci da dama a gaza.
A lokacinda tawagar WHO ta kai ziyarar ganin ido a kan wasu asbitocin sojojin yahudawan suna wa asbitin Indonasiya kofar rago. Haka ma asbitin Kamal Udwan da kuma
Hisam Abu Safiyyah shugaban asbitin Kamal Udwan, sannan yace a kofar ragon da suka yi asbitin a jiya Lahadi ya zuwa lokacin bada wannan labaron falasdinawa kimani 30 suka yi shahada.