Hukumar bada agaji mai kula da yan gudun hijiran Falasdinawa UNRWA ta zargi HKI da rashin kula da dokokin yaki a yankin gaza.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na JMI ya nakalto Philip Lazarine daraktan hukumar ta UNRWA yana fadar haka ya kuma kara da cewa ko wani yaki yana da dokoki in banda yakin Gaza, inda sojojin HKI suke kai hare hare a kan asbitoci, makarantu fararen hula mata da yara da tsoffi. Wato ba ta kiyaye dukkan dokokin yaki.
Philip Lazarine ya kara da cewa HKI bata mutunta ko guda daga cikin dokokin yaki a gaza, kuma hakan a fili yake ga kowa. HKI ta sha kai hare- hare kan Asbitoci kuma tana ci gaba da kaiwa. Ta kashe marasa lafiya ta kashe jarirai ta kuma kashe mutanen da rashin lafiya ta hanasu tashi.
Daga karshe Lazarine ya bukaci kasashen duniya su dai na yin shiru kan ta’adancin da HKI take kaiwa a Gaza.