Ziyarar Da Larijani Ya Kai Pakistan Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kara Dankon Zumunci

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana ziyara da babban sakatare tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya kai kasar a matsayin babban ginshiki a

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana ziyara da babban sakatare tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya kai kasar a matsayin babban ginshiki a alakar dake tsakanin Tehran da kuma Islam Abad , domin ya kara karfafa danganatar dake tsakanin a bangarorin siyasa, tattalin arziki, da kuma tsaro dake tsakanin kasashen makwabtan juna.

Kasashen iran da Pakistan masu makwabtaka da juna za su iya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da yankin gaba ta hanyar yin aiki tare da karfafa dangantaka, musamman a yanayin da ake ciki, domin kasashen biyu baya ga aladu da addini da suka yi tarayyar, a bangaren tarihi ma sun yi nisa.

Babban sakataren tsaron kasar iran Dr Ali larijani ya kai ziyara ne kasar Pakistan na kwanaki 2, inda ya gana da manyan jami’an gwamnati da suka hada da fira minista , shugaban kasar, ministan harkokin waje, shugaban majalisa da kuma kwamandan hafsoshin soji na kasar ta Pakistan.

Kuma ganawar tasu ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi yin aiki tare a bangarorin siyasa, tattalin arziki, tsaro da kuma musayar aladu, dukkan bangarorin biyu suna son kara fadada yin aiki tare a tsaron iyakoki, yaki da ta’addanci ,da dai sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments