Zelesky Ya Ce A Shirye Yaki A Samarda Yankin Da Ba Aikin Soje A Tsakanin Rasha Da Ukraine

Shugaban kasar Ukrain Volodimir Zelesky ya bayyana cewa a shirye yake ya janye sojojinsa daga gabacin kasar Ukraine sannan idan kasar Rasha ma ta amince

Shugaban kasar Ukrain Volodimir Zelesky ya bayyana cewa a shirye yake ya janye sojojinsa daga gabacin kasar Ukraine sannan idan kasar Rasha ma ta amince zasu samar da yankin da babu yaki a tsakanin kasashen biyu idan ana son kawo karshen yakin da ke faruwa a yankin Dambas.

Ya ce idan haka ya faru sojojin kasa da kasa ne zasu kula da yankin da babu yaki, da haka kuma yake fatan za’a kawo karshen yakin na kimani shekaru 3 wanda ya lakume dubban rayukan mutanen kasashen biyu.

Wannan shawara dai wata kofa ce ta kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar, musamman a yankin Dambas inda kasashen biyu suka rasa sojoji da dama. Zeleskiya ta ce Amurka ta amince ta tabbatar  da zaman lafiya a yankin bayan an kawo karshen yaki. Hakama kasashen turai sun yi alkawalin taimaka mata don kawo karshen wannan yakin wanda yajawo asarar rayuka dadukiyoyi da dama.

Ana saran za’a yi irin wannan a yankin da Zaparozia inda Rasha take mamaye da tashar bada wutan lantarki na yankin .

Har yanzun dai kasar Rasha bata bayyana cewa zata  janye daga wadan nan wuraren da Zeleski yake magana a kansu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted