Muhammad Javad Zarif mataimakin shugaban kasa kan al-amura na musamman na kasar Iran, ya bayyana cewa kasar Iran tana da hakkin maida martani kan HKI saboda kissan da ta yi wa shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyyah.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI ta kashe Haniyya da mai gadinsa ne a safiyar ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata bayan ya halarci bukin rantsar da sabon shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan a nan birnin Tehran..
Zarif ya bayyana haka ne a birnin NewYprk na kasar Amurka a lokacinda yake hari da tashar talabijin ta NBC a taron babban zauren MDD na wannan shekarar ta 2024.
Jami’in gwamnatin JMI ya kara da cewa: Iran zata dauki fansa ne saboda keta hurumin kasar wanda gwamnatin HKI ta yi, na kashe bakonta a cikin kasarta.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, kasar Iran tana son zaman lafiya da dukkan kasashen duniya kamar yadda ko wace kasa take so, amma idan an tsokaneta to zata kare kanta.
Kafin haka dai, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta sake bude wani zagayen tattaunawa dangane da farfado da yarjeniyar JCPOA ta shirin nukliyar kasar Iran da kasashen ta abin ya shafa.