Rahotannin da suke fitowa daga birnin Aleppo na kasar Syria sun ce da safiyar yau Lahadi mutanen birnin Aleppo sun fito a dandalin “Sa’adallah al-jabiri’ domin nuna kin amincewarsu da kame wasu mutanen garin da aka yi wanda ake danganawa sabuwar gwamnati karkashin Julani.
Kungiyar Tahrir al-Sham wacce Ahmad Shar, Julani yake jagoranta ta kama wasu mata da suke neman samun ‘yanci, haka nan kuma iyalansu.
Iyalan wadanda aka kama din sun fito dauke da makamai a dandalin na birnin kasar Aleppo suna nun kin amincewa da kama ‘yan’uwansu da aka yi.
Bugu da kari masu Zanga-zangar sun bai wa shugaban gwamnatin ta Syria Julani wa’adin wasu sa’oi kadan akan ya sako musu ‘yan’uwa mata da aka kama.