MSF, Ta Yi Tir Da Harin Isra’ila Da Ya Kashe Ma’aikatanta 2 Gaza

Shi ma Shugaban (WHO), ya bayyana harin a matsayin "abin da ba za a taba amincewa da shi ba."

Kungiyar agaji ta likitoci ta Medecins Sans Frontieres (MSF) ta bayyana rashin jin dadi bayan wani harin Isra’ila ya kashe ma’aikatanta biyu da ke aiki a matsayin masu gadi a wajen wani asibitin lafiya a Gaza a daren Juma’a.

Kungiyar ta (MSF) ta bayyana cewa biyu daga cikin ma’aikatanta, sun rasa rayukansu sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan daya daga cikin cibiyoyinta na kiwon lafiya a yankin Gaza da ke karkashin killacewa.

A wani sako da ta wallafa a shafin X, kungiyar ta bayyana cewa ta shiga cikin “matukar bakin ciki da fushi” game da faruwar lamarin, inda ta siffanta shi a matsayin ” hari kai tsaye kan kungiyar MSF.”

Ta kara da cewa, ya zuwa yanzu, ma’aikatanta 17 ne suka rasa rayukansu a Gaza.

Kungiyar ta bayyana cewa cibiyoyinta na kiwon lafiya suna dauke da alamunta a fili, kuma ta riga ta sanar da sojojin Isra’ila wuraren da suke, wanda hakan ke nuna cewa sojojin sun san wurin.

“Muna nuna goyon baya da juyayi ga iyalai da masoyan abokan aikinmu. Muna kira da a dauki matakin hukunta wadanda ke da alhakin hakan,” in ji kungiyar.

Shi ma Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana harin a matsayin “abin kyama da ba za a taba amincewa da shi ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted