Deby, Zai Jagoranci Kungiyar Kasashen Afirka Ta Tsakiya

Daga cikin manyan kalubalen da ke tattare da shi akwai karfafa hadin kai tsakanin kasashe kungiyar.
Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby

An nada shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby, a matsayin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta tsakiya na wanan karon.

Sabon shugaban ya gaji kungiyar da ke fuskantar kalubalen siyasa, tsaro, tattalin arziki, da na cibiyoyi, ciki har da rikicin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo (DRC), da kuma raunin ciniki tsakanin kasashe membobinta.

Daga cikin manyan kalubalen da ke tattare da shi akwai karfafa hadin kai tsakanin kasashe membobinta, a cikin yanayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankulan diflomasiyya tsakanin Kinshasa da Kigali.

An nada Shugaban Chadi Marshal Mahamat Idriss Déby Itno a matsayin Shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka Ta Tsakiya (ECCAS), inda ya gaji takwaransa na Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, a karshen taron shugabannin kasashe da gwamnatoci karo na 27 da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Malabo, na kasar Equatorial Guinea.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted