228-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare damu a cikin shrimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Almotba (a) da Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da kuma kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku, wasu daga cikin shiar amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) wadanda Mu’awiya dan Abusufyan ya cutar da su ko ya tsoratar da su, banda wadanda ya kashe.
Mun tsaya a inda muke maganar Sasa’atu dan Ssuhan daya daga cikin makusantar Imam Ali(a), wanda ya musulunta a zamanin manzon All..(s) amma bai sami damar zuwa ganinsa ba har ya bar duniya, amma ya zo madina a zamanin khalifa Umar, har ma khalifa ya amince da ra’ayinsa a lokacinda ya nemi ra’ayin mutane kan rabon kudade da yake yi a lokacin. Ya rayu har zuwa lokacinda Imam Aliyu dan Abitalib (a) ya karbi shugabancin al-ummar musulmi har kuma ya zama daya daga cikin mashawartansa(a). Imam (a) yakan aike shi zuwa wasu wurare masu muhimmanci saboda amincewa da hankalinsa da kuma wayonsa.
Munce an ruwaito Imam Assadik (a) yana fada dangane da shi yana cewa, {Ba wandanda suke tare da Amirulmuminina (a) kuma suka san hakkinsa, sai Sasa’atu da wadanda suke tare da shi}.
Sannan mun bayyana cewa, wata rana Imam (a) ya aike shi zuwa wajen Mu’awiya dan Abusufyan a sham dauke da wata wasika zuwa wajensa.
A lokacinda yaje Sham, wata rana ya ji Mu’awiya dan Abu Sufyan ya na yabon kansa, yana cewa ‘Kasa ta Allah ce ni kuma khalifan Allah ne duk abinda na dauka daga dukiyar Allah nawa ne, abinda na bari kuma ya halatta gareni” sai Sasa’atu ya kasa hakuri ya kuma tashi ya mayar masa da martani. Sun ci gaba da jayayya da shin a wani lokaci.
Sannan muka tsaya a inda muke cewa, wata rana Mu’awiya yayi Khuduba a kan mimbarinsa yana cewa.
“Da abu sufyanu ya haifi haifi mutane gaba daya, da zasu kasance masu wayo..
Sai Sasa’atu ya ce: Hakika Adamu wanda ya fi Abusufyan ya haifi mutane akwai masu wayo akwai kuma wawaye a cikinsu.
-Lalle kasarmu tana kusa da filin tashin kiyamah
-Lalle filin tashin kiyama bai yi nisa ga muminina ba, kuma baya kusa da kafiri.
-Lalle kasarmu, kasashe mai tsarki
-Lalle kasa ba abinda yake tsarkake kasa ko ya gurbatata, sai dai ayyuka ne suke tsarkaketa.
-Ya ku bayin Allah ku riki Allah majibincin al-amarinku, ku riki khalifofisa a matsayin sulke ku kare kanku da su.
-Ta yaya, ? alhali an yi watsi da sunnar (manzon Allah(s),), an kuma karya alkawari, don haka ta zama rikici mai cike da rudani a cikin wani yanayi mai cike da duhu, wanda abubuwan da suka faru suka rinjayeta, kuma sakamakon ya rinjayeta.
Sai Mu’awiya ya yi fushi da shi a lokacinda ya ji martaninsa Sasa’atu dan Sawhan. Sai ya tsawata masa yana cewa: Ya Sasa’ad! Ka fada kan awzarka su karya ya fi maka ka bayyana ra’ayinka, da kuma nuna rauninka, Ka gamsu da Al-Hasan bin Ali(a). Na kusan aika masa da sako.
Sai Sasaa ya ce.
Ee na rantse da Allah! Na samesu, mafi girmanku a kakanninsu, mafi kiyaye iyakokin Allah, mafi cika alkawalinku.
Da ka aika masa da zaka sameshi kan kekyawan ra’ayi, mai rikon ra’ayinsa da karfi, zai cutar da kai saboda zafin harshensa, zai kuma dakeka da gaskiyanda ba zaka iya inkarinsa ba.
Mu’awiya ya ji zafin maganarsa, don haka sai ya fara barana gareshi, yana cewa: Wallahi zan hanaka hutu, zan kuma koreka daga nan .
Sai Sasaa yace: wallahi kasa tana da fadi, kuma rabuwa da kai hutu ne. Sai Mu’awiya yace: Na rantse da Allah sai na sa a yanke albashinka. Sai sasaa yace: Idan yana hannuka ka aikata. Lallai arzikina da mafifincin ni’imomina suna hannan wanda taskansa bata karewa, Kyautansa baya yankewa, kuma baya zalunci a hukuncinsa.
Sai Mu’awiya yace: Ka halaka kanka!!.
Sai Sasaa yace: Ka saurara!, bai fadi magana a jahilce ba. Me yasa na cancanci kisa? Kada ku kashe rai wacce Allah ya haramta sai da gaskiya. Wanda aka kashe shi da zalunci, Allah zai yi fushi da wanda ya kashe shi, zai doramasa zunubi, ya shayarda shi tafasashen ruwa, zai konashi a jahannama.
Sai sasaa ya juya ya tafi ya bar Mu’awiya cikin bakin ciki. Amma daga baya ya jefa shi a gidan yari tare da wasu wadanda suke tare da shi. Bayan wani lokaci sai ya shiga wajensa a gidan yarin ya zo gabansu yana cewa: Na hadaku da Allah !! ku fadi gaskiya ! a wajenku, me kuke dauka ta a cikin khalifofi?
Sai Abdullahi dan Al-kawaa daya daga cikinsu ya tashi ya yana cewa: Idan ba ka zo mana da kanka ba da ba zamu yi magana ba, don kai lalle shugabane jabberi mai tsanani. Baka tsoron Allah cikin kissan zababbun bayin sa, sai dai zamu ce: Hakika mun san cewa, kai kana jindadin duniya da yelwa, amma kuntata hanyar lahira, kusa da mutuwa amma baka kula da al-amura mai amfani, kana sanya bata haske ko gaskiya, sannan ka sanya gaskiya bata.
Sai Mu’awiya yace: Lalle Allah ya daukaka mutanen sham da al-amarin shugabanci, mutane wadanda suke kare addininsa, suna barin abinda ya haramta, basu kasance kamar mutanen Iraqi ba, wadanda suke keta hurumin Allah, kuma masu halatta abinda Allah ya haramta.
Sai ibnul Kawaa ya amsa masa da cewa: Ya kai dan Abusufyan, Lalle ga ko wace kalma da ka fada muna da Amsa, muna jin tsoron zaluncinka, idan ka bada dama mu fadi duk abinda muka ga dama da harshemmu zamu kare mutanen kasar Iraki, da harsunammu masu kaifi. Zargin mai zargi ba zai hanamu fadar gaskiya a kan tafarkin Allah ba.
Idan kuma kaki, Lalle zamu yi hakuri sai Allah ya hukunta ya kuma yi mana budi.
Sai Mu’awiya yace: Babu na rantse da Allah ba za’a saki harshenka ka fadi abinda kaga dama ba.
Sai Abdullahi yayi shiru, sai Sasaa ya dauka, yana cewa: Ya kai dan Abusufyan, kayi magana kuma ka cika bakinka. Baka takaita abinda kake nufi da maganarka ba, amma al-amarin ba kamar yanda ka ambace shi ba. Ta yaya khalifanci zata kasance ga wanda ya hau kan mutane da karfi?, ya daukaka a kansu, ya mamaye al-amuransu ta hanyoyin da basu dace ba, tare da amfani da karya da makirci?.
Amma na rantse da Allah! Baka da wani tasiri a ranar badar bakayi yi duka da takobi ba, baka yi harbi da mashi ba, masilinka kamar mutum ne wanda bai da wani amfani.
Kuma kai da babanka kun kasance cikin wadanda suka zo yakar manzon Allah (S), kuma ka san cewa kana daga cikin yentaccen bawan manzon All..(s) dan yentaccen bawansa a ranar fatahin Makka. Ta yaya khalifanci zata dace da kai?.
Sai Mu’awiya yayi fushi, sai ya ce: Na sanya afwa da dauriya maimakon laifin da kuka yi mana, na sanya Afwa duk da cewa ina da iko a kanku, kuma wani nau’ii ne na karamci, wallahi da na kasheku.
Shi sasaa dan Sauhan dai yana daga cikin mutanen da Imam Al-Hassan (a) ya nemammasa afwa daga Mu’awiya, ya ci kada da wahalar da shi, amma yaki amsa bukatarsa dangane da shi, yaki yayi masa afwa. Ya wahalar da shi, a jefa shi a gidan yari.
Sannan wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, mu’awiya ya umurci Mughira dan shuba, ya kori sasaatuh dan Sauhan daga Kufa, da shi da wasu mutanensa zuwa, Aljazeerah, ko kuma Bahrai, ko kuma wasu wurare, inda suka nisantar da su daga mutane har suka mutu a tsare a can.
Sai kuma Adiy dan Hatam Attaee, Adi yana daga cikin manya manyan mutane a Kufa, yana da daukaka a jalihiyya, sannan mai daukaka a musulunci. Mahaifinsa shi ne Hatamut Taaee wanda ake buga misali da shi a yawan karamci da kyau, bayan mutuwar mahaifinsa shi ne shugaban kabilarsa Attai, wadanda suke tsakanin duwatsu biyu, ya musulunta a hannun manzon All..(s). Don haka shi sahabin manzon All..(s)ne, daga baya mutanen kabilarsa suka musulunta saboda shi. Bayan da Imam Ali (a) ya karbi shugabancin Al-ummar musulmi, Adi dan Hatam ya kasance tare da shi a yakin Jamal da Siffin kuma yayansa guda uku sun yi shahada a yake yake tare da Amirulmuminina (a). Bayan shahadar Imam Ali (a) ya kasance tare da mutanensa da Imam Al-Hassan(a).
Bayan da Imam Alhassan (a) ya mika shugabanci, ga Mu’awiya dan Abusufyan, Adi da mutanensu sun ci gaba da kasancewa a Kufa, mun kawo maganarsa a lokacinda muka yi maganar Abdullahi dan Khalifah Attaee, da kuma yanda ya ki amincewa ya bada shi ga Ziyada dan Sumaiya ya kashe shi.