Tunisia: Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama Sun Bukaci Bayani

Babbar kungiyar kare hakkin bil’adama mafi girma a kasar Tunisa tare da wasu kungiyoyin sun bayyana damuwarsu da yanda fursinoni musamman fursinonin siyasa suke yawan

Babbar kungiyar kare hakkin bil’adama mafi girma a kasar Tunisa tare da wasu kungiyoyin sun bayyana damuwarsu da yanda fursinoni musamman fursinonin siyasa suke yawan mutuwa a gidajen yari a kasar.

Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya bayyana cewa, firsinoni kimani 30 ne suka mutu a gidajen yara a cikin yan watannin da suka gabata a kasar Tunaiya.  Don haka sun bukaci gwamnatin kasar ta yi bayani ta kuma bada dama a ziyarci gidayen yarin.

Labarin ya kara da cewa, har yanzun gwamnatin kasar bata bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu a gidajen yarin kasar sanadiyyar tsakanin zafi karancin ruwa da kuma katsewar  want lantarki a cikin yan watan da suka gabata ba. Amma

Bassem Trifi shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar Tunisia ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa, akwai cinkoso mai yawa sannan rashin tsabta da kula da rashin kula da dokokin kiwon lafiya suna nan a mafi yawan gidajen yarin kasar, musamman a cikin yanayin zafin da ake fama da shi a cikin yan makonni da suka gabata.

Wannan ya yi sanadiyyar mutuwar Fursinoni da dama , Tarif ya ce kungiyarsa tana da labarin mutuwar mutanen akalla 30  a gidajen yarin kasar ya zuwa yanzu kuma lallai ne gwamnati ta fito ta yi nkarin bayani a kan wadannan mace macen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted