Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump

Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana

Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a birnin NewYork.

Magajin garin ya bada misali da cewa a halin yanzu yara kimani 100,000 ne a birnin NewYork basa da wurin kwana shekaru 9 a jare. Mamdani yace yana nufin yadda shugaban Trump yake kashe biliyoyin dalar Amurka kan tallafawa HKI a yakin da take da kasashen larabawa a yayinda ana bukatar wadan nan kudade a cikin gida.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted