Kakakin Rundunar Sojin Yemen ya sanar da cewa: Mutane da dama ne suka yi shahada tare da jikkata a harin da Saudiyya ta kai kan kasuwa a gundumar Ta’iz
Kakakin Rundunar Sojin Yemen Yahaya Sari’e ya sanar da cewa: Wani jirgin yakin kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai hare-hare sau uku a wata kasuwa da ke lardin Ta’iz, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama, ciki har da mata da yara tare da raunata wasu na daban.
Kamfanin dillancin labaran Mehr, wanda ya ambato kamfanin dillancin labaran Al-Masirah, ya ruwaito cewa: Janar Yahaya Sari’e, kakakin rundunar sojin Yemen ya sanar da cewa: Wani jirgin saman yakin Saudiyya kirar F-15 ya tashi da karfe 7:10 na safe a yau daga sansanin jiragen sama na Khamis Mushait kuma ya kai hare-hare sau uku inda ya nufi kasuwar Al-Hadara a gundumar Al-Waziyah da ke lardin Taiz.
Mai magana da yawun ya jaddada cewa: Harin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai kan kasuwar Al-Hadara kuma ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.
Sare’i ya nuna cewa wadannan munanan laifuka za a mayar da martani mai tsauri kansu, Da yardan Allah.