Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa a Yemen, ta yi Allah wadai da hare-haren sama na Saudiyya kan gidajen jama’a a kauyen Ash Sharyah da ke gundumar Bani Hushaysh dake gabashin Sana’a, wanda ta bayyana a matsayin “laifi na yaki.”
Hukumar ta yi kira da a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da na kasa da kasa domin gudanar da bincike kan ayyukan zalunci da Saudiyya ke yi wanda ya shafi kasuwanni da unguwannin fararen hula, bayan da aka kashe mutane da dama, galibi mata da yara, a hare-haren sama da aka kai kusa da babban birnin kasar, Sana’a.
A cikin wata sanarwa, Mai sa ido kan kare hakkin bil’adama na kasa da kasa a Sana’a ya jaddada cewa kisan da aka yi a kauyen Ash Sharyah kisan kiyashin ne da Saudiyya ke yi wa al’ummar Yemen.
Kwamitin ya kara da cewa hare-haren Saudiyya sun kashe dubban fararen hula tare da lalata cibiyoyin fararen hula da kayayyakin more rayuwa a larduna daban-daban na Yemen.
Tashar talabijin ta al-Masirah ta Yemen ta ruwaito a ranar Asabar cewa akalla mutane 27, ne galibi mata da yara, suka mutu, kuma sama da 36 sun jikkata a hare-haren jiragen saman Saudiyya kusa da Sana’a.
Kakakin rundunar sojan Yemen, Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana a cikin wata sanarwa a shafin sada zumunta na X cewa, a cikin da suka gabata, sojojin Saudiyya sun kai hare-hare ta sama da makamai masu linzami guda 105 a birnin Sana’a da wasu larduna bakwai na Yemen.
Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wadanda yawancinsu mata da yara ne.
A ranar 20 ga watan Yuli, gwamnatin Sana’a ta sanar da kakaba takunkumin hana zirga-zirgar ta hanyoyin ruwa kan Saudiyya, wanda ta bayyana a matsayin martani ga “takunkumi na zalunci da danniya” da aka kakaba wa Yemen tsawon kusan shekaru 12.