‘Ya’yan Jagoran juyin juya halin Musulunci da wakilansa sun ziyarci majinyatan kasar Labanon wadanda aka kawo su jinya asibitocin birnin Tehran na Iran
‘Ya’yan Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da wakilansa sun ziyarci wasu daga cikin wadanda suka jikkata da kuma mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon da aka kawo su jinya a asibitocin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.
Wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka da nakasa sakamakon hare-haren wuce gona da irin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar Lebanon a baya-bayan nan an kawo su Iran domin ci gaba da kula dalafiyansu, kuma suna birnin Tehran domin kammala aikin jinya, sannan sun fito ne daga kungiyoyin gwagwarmaya daban-daban, ciki har da jarirai, kananan yara gami da samari a cikinsu. Majinyatan sun tarbi wakilan Jagoran juyin juya halin na Musulunci cikin yanayin nuna jin dadinsu duk da radadin raunukan da suka samu. Kamar yadda ‘ya’yan Jagoran juyin juya halin Musulunci da jami’an Iran suka bi diddigin yadda ake kula da majinyatan, kuma aganawarsu da marasa lafiyan suka isar musu da sakon Jagoran da gaisuwarsa gare su gami da yimusu fatan samun sauki da nimka musu ladar jinya.