An ci gaba da gano karin gawaki sanadiyyar zeizeyar kasa da ta auku a lardin Bulambuli na kasar Uganda a ranar Laraban da ta gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ ya nakalto kakakin kungiyar bada agaji ta Red-Cross ta kasar Uganda, Irene Kasiita yana fadar haka a jiya Jumma’a. Kasiita ya kara da cewa an gano gawakin mutane guda hudu a jiya Jumma’a a yayinda daya daga cikin wadanda suke jinya a asbita Mbale kuma ya rasu. Wanda ya kawo adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar zeizeyar kasar zuwa mutane 20.
A ranar Laraban da ta gabata ce, laka da ke kan tsaunuka a yankin Bulambuli, mai tazaran kilomita 280 daga gabancin birnin Kampala babban birnin kasar Uganda, ta zeizaye a cikin dare, ta kuma binne kauyuka kimani 7 saboda yawan ruwan sama a yankin.
Jami’an gwamnatin a yankin sun bayyana cewa zeizeyar kasar ta lalata gidaje 125. Kuma ta shafi mutane 750 ne, Banda haka mutane 216 suna samun mafaka na wucin gadi a wata makaranta a yayinda wasu suka koma gidajen yan’uwa da abokan arziki. Labarin ya kara da cewa ana ci gaba da neman masu sauran numfashi, duk da cewa ana ci gaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin.