Yawan Falasdinawan Da Suka Yi Shahada Sun Haura 37,000 Tun Daga Ranar 7 Ga Watan Oktoban Bara

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri a Gaza ya haura mutane dubu 37,000 Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta watsa rahoton

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri a Gaza ya haura mutane dubu 37,000

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun aiwatar da kisan kiyashi kan iyalai 4 a Zirin Gaza da suka kunshi shahidai 34 da jikkatan wasu 71 na daban kuma an garzaya da su zuwa asibitoci.

Don haka adadin Falasdinawa da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kashe tun daga fara kai hare-hare kan Zirin Gaza a ranar bakwai ga watan Oktoban bara ya kai shahidai 37,266 da jikkatan 85,102.

Ofishin watsa labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa: Adadin yaran da suka yi shahada tun farkon hare-haren sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a zirin Gaza ya kai yara 15,694, baya ga kananan yara 34,000 da suka samu raunuka tun farkon harin.

Ofishin watsa labarai na gwamnati yayi nuni da cewa: Yara 3,600 ne suka bace a karkashin baraguzan gine-ginen da suka rufta, sakamakon hare-haren da aka kai kan yankin, inda ya tabbatar da cewa akwai yara akalla 200 daga Gaza da sojojin mamaya suka yi awungaba da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments