Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammad Bin Salman ya bayyana wa wakilan Amurka hadarin fuskantar kisan gilla
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman ya bayyana wa dan majalisar dokokin Amurka hadarin da yake fuskanta na aiwatar da kisan gillakansa, a cewar shafin yanar gizo na Politico na Amurka.
A cewar jaridar Politico, Bin Salman ya shaidawa dan majalisar cewa yana jefa rayuwarsa cikin hadari wajen kokarin cimma wata babbar yarjejeniya da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila wadda ta hada da daidaita alakar Saudiyya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
A cewar shafin, akalla sau daya, Bin Salman ya kirayi Anwar Sadat, shugaban Masar da aka kashe bayan kulla yarjejeniyar daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ya tambayi abin da Amurka ta yi don kare Sadat daga haqtsarin da yake fuskanta.
A yayin da yake tattaunawa game da barazanar da yake fuskanta, Bil Salman ya bayyana bukatar gudanar da shawarwari da kulla yarjejeniyar Gaza da ta hada da hakikanin hanyar kafa kasar Falasdinu mai cin cikakken ‘yancin kai, musamman bayan yakin Gaza da ya haifar da karuwar fushin Larabawa kan haramtacciyar kasar Isra’ila.