Sojojin HKI sun sanar da cewa jiragensu na sama sun yi nasarar kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo daga Yemen da safiyar yau Talata.
Kungiyar agaji a can HKI ta ce mutane 20 ne su ka jikkata sanadiyyar turmutsutsu zuwa inda za su buya bayan kadawar jiniyar gargadi.
Lokaci kadan gabanin wannan, sojojin na HKI sun ambaci cewa sun kakkabo wani jirgin sama maras matuki da aka harbo shi daga Yemen, gabanin ya shiga cikin sararin samaniyar Falasdinu dake karkashin mamaya.
Janar Yahya Sari wanda shi ne kakakin sojojin Yemen ya sanar da cewa sun kai hari da makami mai linzami da kuma jirgin sama maras matuki akan cibiyoyin HKI masu muhimmanci da su ka hada yankin Askalan, da kuma Yafa dake tsakiyar Tel Aviv.
Janar Sari ya kara da cewa, sojojin Yemen za su cigaba da kai wa HKI hare-hare har zuwa lokacin da za a kawo karshen yaki akan Gaza da kuma dauke wa yankin takunkumi.
Tun daga lokacin da HKI ta shelanta yaki akan Falasdinu a 2023 ne dai sojojin Yemen su ka shiga taya Falasdinawa fada, ta hanyar harba wa HKI makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.
A ranar Asabar din da ta gabata ma dai sojojin na Yemen sun kai wa tsakiyar Tel Aviv hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic” da su ka bai wa sunan ( Falasdinu 2). Saukar makamin ya rusa ilahirin ginin da ya fadawa da kuma sauran gine-ginen da suke kusa da shi. Haka nan kuma ya jikkata mutane kusa 30 kamar yadda kafafen watsa labarun HKi su ka ambata.