‘Yan gwagwarmayar Jenin sun bayyana cewa: Sun amince da shirin sulhu da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa
‘Yan gwagwarmayar sansanin Jenin da ke da alaka da Dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul- Islami ta bayyana cewa sun amince da wani shiri na sulhu da hukumar cin gashin kan Falasdinawa da nufin kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa.
Sun kara da cewa, a cikin wata sanarwa da suka fitar a jiya Talata, “Sun amince da wani shiri da zai tabbatar da haƙƙin su na ci gaba da gwagwarmaya da ‘yan mamaya da dakile muggan laifukansu da suka hada da cin zarafin wurare masu tsarki da keta hurumin yankunan Falasdinawa da kuma cin zarafin al’ummar Falasdinu.
Tun a watan da ya gabata ne jami’an tsaron Falasdinu ke ci gaba da kai farmakin soji kan sansanin Jenin bisa da’awar neman kame wadanda suke keta dokokin kasa, yayin da bangarorin Falasdinawan suke zargin jami’an tsaron hukumar ta Falasdinawa da cika muradun yahudawansahayoniyya na murkushe ‘yan gwagwarmaya.