Search
Close this search box.

‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Suna Ci Gaba Da Kalubalantar Sojojin Yahudawan Sahayoniyya

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da jarumtakar kalubalantar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila a Gaza Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da jarumtakar kalubalantar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila a Gaza

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun watsa wasu hotuna da mayakanta suka kaddamar da hare-hare kan hedikwatar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Netzarim a tsakiyar yankin zirin Gaza ta hanyar harba makaman roka.

Mayakan Al-Qassam sun kai hare-haren ne kan hedkwatar rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Netzarim a shiyar yammacin Gaza da makamai masu linzami masu cin gajeren zango na mm 114, a cewar sanarwar.

A ranar Asabar da ta gabata ma, dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun sanar da kai wani harin kwantan bauna kan tawagar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, wanda ya yi sanadin halakar wasu daga sojojin tare da raunata wasu na daban a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza. Har ila yau a jiyan dakarun na Izzuddeen Al-Qassam sun sanar da cewa: A safiyar ranar Arafa, mayakansu sun kai wani kazamin harin kwantan bauna kan motocin sojojin yahudawan sahayoniyya da suke kutsawa cikin yankin Saudiyya da ke Tal al-Sultan a yammacin birnin Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments