An kashe wani kwamandan dakarun yahudawan sahayoniyya a yankin Al-Zaytoun da ke kudancin Gaza
Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar da halakar wani jami’insu sakamakon fashewar wani bom a yankin Al-Zaytoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza.
Kakakin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Kwamandan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila mai suna Yotam Itzhak Peled dan shekaru 34 a duniya, kuma ya kasance kwamandan dakarun yahudawan sahayoniyya ‘yan kwana-kwana, kuma yana aiki ne a fannin gabatar da dabarun yaki.
Gidan rediyon soji haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana yadda aka kashe jami’in da cewa: Wata rundunar sojan haramtacciyar kasar Isra’ila dake kula da dabarun yaki ta fuskanci fashewar wani bom a lokacin da ta shiga yankin Al-Zaytoun, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in da jikkata wasu sojojin na daban.
Gidan rediyon ya kara da cewa, fashewar bom din ta biyo bayan ficewar wasu ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa ne daga wani gini da ke kusa da wurin, inda suka bude wuta kan sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila kafin su janye daga wurin.
Kamar yadda ‘yan gwagwarmayar suka yi nasarar kashe wasu jami’in sojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yau, inda adadin sojojin da suka halaka daga sojojin mamaya da tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kakan gida suka karu.
Har ila yau, a cewar cibiyar da ke kula da harkokin sojin Isra’ila ta Akka ta yi nuni da cewa: An kashe wasu tsagerun yahudawan sahayoniyya guda biyu a wani harin wuka da aka kai a Holon da ke kusa da birnin Tel Aviv.