Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas sun lashi takwabin ganin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ba su koma ga iyalansu rayayyu daga Gaza ba
Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da kai hare-hare kan sojojin kafa na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Al-Shoka da ke gabashin birnin Rafah a kudancin Zirin Gaza, inda suka kashe tare da raunata sojoji masu yawa.
Bayan da rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da fara kwashe sojojinta zuwa yankin arewaci, bisa la’akari da cewa sun kammala mafi yawan ayyukan da suke gudanarwa a Zirin Gaza, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun zafafa kai hare-hare kan sojojin mamaya musamman a birnin Rafah da ke kudancin Gaza da unguwar Tal al-Sultan.
A yayin da ake ci gaba da samun tabarbarewar al’amura a cikin kasar Lebanon da kuma bangaren arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun yanke shawarar yin amfani da damar wajen kara janyo munanan hasarori musamman na rayukan sojojin yahudawan sahayoniyya. Rundunar ta Al-Qassam ta sanar da cewa mayakanta sun kai hari kan wata tankar yaki ta Merkava a yankin Al-Shuka da ke gabashin Rafah, sannan kuma sun harba makamai masu linzami kan sojojin kafa na haramtacciyar kasar Isra’ila, inda suka tabbatar da kashe sojojin tare da jikkata wasu na daban.