Dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul-Islami sun kai hari kan wani gida da sojojin mamayar Isra’ila na musamman suka mayar da shi matsuguninsu a Jabaliya
Dakarun Sarayal-Quds, bangaren sojin kungiyar Jihadul- Islami, sun wallafa wasu hotunan da mayakansu suka kai farmaki kan wani gida da sojojin mamayar Isra’ila na musamman suka mamaye shi a matsayin matsuguninsu a sansanin Jabaliya.
Sarayal-Quds sun wallafa faifan bidiyon, inda a cikin aka ga yadda suka nufi wata motar yakin ‘yan sahayoniyya ta Merkava da makamai masu linzami da ta shiga tsakiyar birnin Beit Lahiya, kuma suka yi nasarar tarwatsa ta.