‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun yi luguden bama-bamai a kan sansanonin sojojin mamayar Isra’ila tare da kakkabo jiragen saman yaki marasa matuka ciki guda 3
‘Yan gwagwarmayar rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, sun sanar da kakkabo wasu jiragen saman yaki marasa matuka ciki guda uku mallakin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a gabashin birnin Rafah. Sanarwar da Rundunar Sojin ta fitar a jiya Juma’a ta ce: ‘Yan gwagwarmayar Al-Qassam sun yi nasarar kakkabo wasu jiragen saman marasa matuka ciki guda uku na ‘yan sahayoniyya a yayin da suke gudanar da aikin leken asiri a unguwar Al-Geneina da ke gabashin birnin Rafah a shiyar kudancin Zirin Gaza.
A cikin wani rahoto na daban, Dakarun Al-Qassam sun sanar da cewa: sun yi luguden wuta kan sojojin mamayar Isra’ila da suka kutsa cikin yankin Al-Barid da ke sansanin Jabaliya a shiyar arewacin Zirin Gaza ta hanyar amfani da manyan bindigogi.
A nasu bangaren kuma, dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul-Islami sun nuna faifan bidiyo na wani hari da mayakansu suka kai da makami masu linzami kan ayarin motocin sojoji mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suka yi kutse a yankunan Falasdinawa a birnin Rafah.