“Yan Gwagwarmaya Sun Kai Hari Akan Motocin Sojojin Mamaya Da Su Ka Yi Kuste Cikin Khan-Yunsu

Gwagwarmayar musulunci a Gaza ta kai hari akan wani ayarin  motocin sojojin mamaya da su ka kutsa cikin yankin Khan-Yunus, inda su ka yi musu

Gwagwarmayar musulunci a Gaza ta kai hari akan wani ayarin  motocin sojojin mamaya da su ka kutsa cikin yankin Khan-Yunus, inda su ka yi musu asara ta kayan aiki da sojoji.

An kai wannan hari ne dai adaidai lokacin da yakin Gaza ya cika kwanaki 292 ana yi, wana ya ci rayuka kusan 40,0000 da jikkata wasu dubun budabar Falasdinawa.

Sojojin mamayar HKI sun ce, biyu daga cikinsu sun jikkata sanadiyyar wannan harin da aka kai musu,kuma sun fito ne daga rundunar “Gaf’ani”.

A gefe daya mayakan “Izzudduin al-Kassam’ sun sanar da rusa Tanar Mirkaba ta hanyar amfani da makamin “Shwaz” a garin  Banmi-Suhaila dake gabashin birnin Khan-Yunusu a kudancin Gaza.

A can garin Rafah kuwa mayakan na “Kassam” sun tarwasa wani gida da sojojin HKI su ka shiga ciki ta har tashin bama-baman da su ka sanya a ciki.

 A gefe daya, a cigaba da aiki tare da ake yi a tsakanin kungiyoyin na gwgawarmaya, “Kata’ibu Shhada’u Aqsa, da kata’ibu Shadin Abu Ami Mustafa, sun sanar da kai harin hadin gwiwa akan sansanin sojan mamaya na “Za’im’ ta hanyar harba makamai masu linzami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments