Search
Close this search box.

‘Yan Gwagwarmaya Sun Halaka Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Hudu A Zirin Gaza

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar da halakar sojojinsu hudu a shiyar kudancin Zirin Gaza Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar a safiyar

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar da halakar sojojinsu hudu a shiyar kudancin Zirin Gaza

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar a safiyar yau talata cewa: An kashe sojojinsu hudu a fadan da ake gwabzawa a kudancin Zirin Gaza, a daidai lokacin da hare-haren yahudawan sahayoniyya kan Gaza suka shiga wata na tara a jere.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Quds Al-Arabi cewa: A cikin wata sanarwa da sojojin yahudawan sahayoniyya suka fitar sun tabbatar da halakar sojojinsu guda hudu a yakin da ake gwabzawa a shiyar kudancin Gaza, ba tare da bayar da cikakken bayani kan yanayin mutuwarsu ba.

Majiyar sojin ta haramtacciyar kasar ta Isra’ila ta kara da cewa: Baya ga halakar sojojin hudu, wasu sojoji 11 na daban kuma sun jikkata sakamakon mummunar fashewar wasu bama-bamai da suka kai ga rugujewar wani katafaren gini a kan bangaren sojin Givati da ke yaki a birnin Rafah. Daga cikin sojojin, akwai guda biyar da raunukansu suka yi muni, yayin sauran kuma suka samu raunuka matsakaita.

Kamar yadda a jiya litinin, Dakarun Izzudde4en Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da kashe wasu sojojin yahudawan sahayoniyya tare da raunata wasu na daban, sakamakon tayar da wasu bama-bamai a wani gida da sojojin suka fake a ciki a birnin Rafah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments