Yamen Ta Soki Kasashen Birtaniya Da Amurka Da Tsoma Baki Kan harkokin Kasarta

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Yamen ta yi tir da matakin da kasashen birtaniya da Amurka suka dauka na sukar hukumcin kisa da aka yanke

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Yamen ta yi tir da matakin da kasashen birtaniya da Amurka suka dauka na sukar hukumcin kisa da aka yanke wa wasu yan leken asiri bayan kama su da laifi, tace bata amince da wannan mataki ba kuma tsoma baki ne a harkokin cikin gidanta.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar yamen ta bayyana cewa ma’aikatar sharia ta kasar tana da cikakken yanci kuma tuni ta yanke hukumcin kisa kan wadanda aka kama da yi wa kasashen waje leken asiri a kasar

Haka zalika ta ce duk wata kasa da tace za ta dauki mataki kan wannan hukumci Amurka ce ko birntaniya to za ta dauke shi matsayin shiga shugalarta ne, kuma ba za ta amince da shi ba, domin a yamen ma’aikatar harkokin cikin gida da ta sharia suna da yanci.

Daga karshe ta nuna cewa bai kamata Amurka tayi Magana kan adalci ko kare hakkin bil adama ba,domin hanunta yana cike da jinanen mutane a sassa daban daban na duniya,musamman a yankin gaza inda Amurka take goyon bayan isra’ila wajen kashe fararen hula sama da 70,000 tun daga oktoban shekara ta 2023 zuwa yau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments