Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sun kai hari a filin saukar jiragen saman birnin Riyadh a matsayin daukar fansa na hare-haren Saudiyya a Yemen.
Janar Sari, ya kuma bayyana cewa; sojojin na yemen sun yi amfani da makamin da ya dace domin harbo jirgin yakin Saudiyya a samaniyar birnin Ta’iz.
Janar Sari ya kuma ce; Biranen Makka da Madina ne kadai aka yi wa togiya ba za a kai wa hari, amma idan ba su ba, dukkanin garuruwan Saudiyya filayen dagar mayar da martani ne.
Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai wasu munanan hare-hare kan kasar Yemen tare da kashe mutane fiye da goma
Rahotonni sun watsa labarin cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare ta sama masu tsanani a yankuna daban-daban na Yemen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Yemen 13 da kuma jikkata wasu na daban.
Kamfanin dillancin labaran Mehr, wanda ya nakalto daga kafar Al-Masirah na Yemen ya bayyana cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare kan yankunan Ali al-Amri da Bab al-Mandab a Dhubab sau shida, da kuma yankin Haifan sau uku.
Gundumar Sa’ada, a arewacin Yemen, hare-haren jiragen saman Saudiyya sun kwashe ‘yan mintuna suna luguden wuta kan gidajen jama’a. Saudiyya ta kuma kai hari kan gonaki da gidaje a garuruwan Sahar da Saqin a lardin Sa’ada da makamai masu linzami.