Falasdinawa 82 ne suka yi shahada a birnin Rafah cikin ‘yan sa’o’i bayan hukuncin kotun kasa da kasa
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila” ta aiwatar da wani sabon kisan gilla a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, kasa da sa’o’i 30 bayan wani mummunan kisan gilla na farko da ta yi a kusa da rumbun adana kayayyaki na hukumar kula da harkokin Falasdinawa ta UNRWA, yayin da adadin shahidai a birnin ya karu zuwa 82. cikin kasa da sa’o’i 100 daga matakin da kotun shari’a ta kasa da kasa ta yanke na dakatar da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kaiwa kan Falasdinawa.
A cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta kara da cewa: An tattara bayanan mutuwar fararen hula 7 da suka hada da mata 4, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka sake kai hare-hare kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Tal al-Sultan da ke arewa maso yammacin Rafah.
Rahotonni sun yi nuni da cewa: Sabbin hare-haren sun faru ne a yankin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 45 da suka hada da yara 9, mata 12, da kuma tsofaffi 3.