Search
Close this search box.

Yahudawa Suna Ci Gaba Da Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnatinsu

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta shiga rudani sakamakon yadda zanga-zangar adawa da gwamnatin fira minista Netanyahu ta kara kamari Gidan rediyon sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta shiga rudani sakamakon yadda zanga-zangar adawa da gwamnatin fira minista Netanyahu ta kara kamari

Gidan rediyon sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya watsa rahoton cewa: Jami’an tsaron yahudawan sahayoniyya sun kame masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Fira minista Benjamin Netanyahu guda bakwai a yankuna daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila, a yayin zanga-zangar da aka yi a gaban gidajen ministocin yahudawan sahayoniyya domin neman a gaggauta kammala yarjejeniyar musayar fursunoni da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa bayan sake komawa fagen tattaunawar da aka yi kwanaki a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar.

A sa’o’i kadan da suka gabata, an kaddamar da zanga-zanga da safe a garuruwa daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila, don neman cimma yarjejeniyar musayar fursunonin, yayin da wani kuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa kashi 54% na yahudawan sahayoniyya sun yi imanin cewa ana ci gaba da yakin ne a Gaza saboda neman cimma ra’ayin siyasa na Fira Minista Netanyahu.

Masu zanga-zangar sun rufe babban titin Ayalon da ke tsakiyar birnin Tel Aviv, inda suka bukaci a gudanar da a hanzarta gudanar da zabe a haramtacciyar kasar Isra’ila domin kawo karshen shugabancin Netanyahu, inda suka daga tutar da ke dauke da cewa: “Gwamnatin rushe-rushe ta ishe su”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments