Yahudawan Sahayoniyya 3 Ne Suka Halaka Yayin Da Wasu 10 Suka Jikkata A Qalqilya

Yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida uku 3 ne suka halaka kuma wasu fiye da 10 nadaban suka jikkata sakamakon harbin bindiga da aka kai musu

Yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida uku 3 ne suka halaka kuma wasu fiye da 10 nadaban suka jikkata sakamakon harbin bindiga da aka kai musu ashiyar gabashin garin Qalqilya

Rahotonni sun watsa labarin cewa: ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kai wani samame kan kauyen Al-Funduq da ke gabashin garin Qalqilya a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye a safiyar yau Litinin, inda suka halaka yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida guda uku tare da jikkata wasu fiye da 10 na daban.

Majiyoyin cikin gidan Falasdinu sun rawaito cewa: ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawan sun bude wuta ne kan wata motar bas da take dauke da yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a kusa da kauyen Al-Funduq da ke gabashin Qalqilya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta yahudawan sahayoniya ta tabbatar da cewa, adadin wadanda harin ya halaka sun kai 3, yayin da wasu 6 kuma suka jikkata, daya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, yayin da wasu majiyar rundunar sojojin mamayar Isra’ila ta sanar da cewa, adadin wadanda suka jikkata a harin da aka kai a Qalqilya ya karu zuwa 10.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments