Dangi da iyalan yahudawa da aka yi garkuwa da su a Gaza sun gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar Knesset ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila, inda suka bukaci gwamnatin Netanyahu ta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kamar wadda aka cimma da Lebanon.
Masu zanga-zangar sun toshe kofar shiga ofishin Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ke cikin ginin majalisar Knesset na wani dan lokaci a ranar jiya Laraba, kamar dai yadda kafafen yada labarai na Isra’ila suka ruwaito.
Masu zanga-zangar dai sun bukaci Netanyahu ya gana da su tare da cimma yarjejeniyar musayar fursunoni domin a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza, wadanda aka kiyasta cewa adadinsu ya kai 101.
Wannan zanga-zangar na zuwa ne kwana guda bayan da majalisar ministocin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Lebanon.
Eli Albag, dan uwan daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ya ce kamar yadda Netanyahu ya amince da tsagaita bude wuta don dakatar da yaki da Lebanon, ya kamata ya yi hakan a Gaza.